Gwamnatin tarayya ta umarnin buɗe makarantu a faɗin tarayyar ƙasar nan biyo bayan rahoton kwamitin yaƙi da cutar Korona ya bayar.
Shugaban kwamitin yaƙi da cutar Korona na fadar shugaban ƙasa, Dakta Sani Aliyu ya bayyana haka a jawabin kwamitin na ranar Alhamis.
“Makarantun raino da firamare da sakandare da manyan makarantu da cibiyoyin ilimi su fara shirye-shiryen buɗewa.”
https://dimokuradiyya.com.ng/korona-har-yanzu-babu-ranar-buɗe-makarantu-ministan-ilimi/
Sai dai ya ce, “Muna shawartar da a yi cikakken bincike domin tantance yayanin haɗari domin tabbatr da cewa dukkanin makarantu sun tanadi dukkanin kaya da matakan kariya da kuma tabbatar da bin dokokin”.
A watan Maris aka rufe makarantu a Najeriya bayan ɓullar cutar Korona kafin a sake buɗewa a ranar 4 ga Agusta ga ɗalibai masu rubuta jarabawar kammala firamare da kuma ƙarama da babbar sakandare.
“Wuraren raino makarantu za su kasance a rufe har sai an gama tantance yanayi haɗarin.
“Idan aka tashi buɗe makarantun, dole ne ya zama mataki-mataki domin kawar da barazanar ga al’umma da mutane masu rauni da ke iya kamuwa da cutar”, inji Dakta Sani.