Gwamnatin tarayya ta ce za ta buɗe jigilar jiragen sama na ƙasa da ƙasa daga ranar 29 ga watan Agusta da zamu shiga.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a yammacin Litinin 17 ga Agusta 2020 ta shafinsa na Twitter.
“Za mu fara da Legas da Abuja kamar yadda muka yi a lokacin buɗe sufurin jirage na cikin gida. Nan gaban za a sanar da tsare-tsaren da kuma matakan da aka tanada. Muna godiya bisa haƙurin da kuka nuna”, cewar Sirika.
https://dimokuradiyya.com.ng/korona-za-a-buɗe-filayen-tashin-jiragen-saman-ƙasar-nan/
Wakilinmu ya ruwaita ministan na sanar da haka a lokacin taron jawabin kwamitin shugaban kasa kan yaƙi da cutar Korona.
Ya ce idan aka buɗe filayen bayyan mako biyun masu zuwan, za a ci gaba da bin sauran matakan kariya da suka hada da bayar da tazara da dangoginsu.
Tun a watan Fabrairu gwamnatin tarayya ta rufe dukkannin tafiye-tafiyen jiragen sama da na ƙasa domin daƙile yaɗuwar cutar a faɗin ƙasar nan.