• jihar Yobe ta sami kyautar motocin kashe Gobara daga gwamnatin Tarayya.
• Gwamnan jihar Mai Mala Buni ya yaba da wannan kyauta.
• Ya Kuma bukaci Hukumar da ta ciga ba da bai wa takwarar ta ta jihar Yobe horo domin kare rayukar da dokiyoyin al’uma.
Hukumar kiyaye afkuwar gobara ta kasa, ta bai wa takwararta ta jihar Yobe kyautan sabbin motocin kashe gobara.
Lokacin da ya ke amsan sabbin motocin a fadar gwamnatin jihar dake Dammaturu, daga hukumar kiyaye afkuwar gobara ta kasa, Dakta Liman Ibrahim A. Ibrahim ya ce, Gwamnan jihar Mai Mala Buni ya bayyana gyauyar amastayin abun alfahari, wanda ka iya magance dukkannin nau’in gobara a fadin jihar baki daya.
Gwamna Buni ya ce, samun motocin zai taimaka wa gwamnatin jihar matuka, wurin ta kaita kai dauki a dukkannin fadin jihar, idan bukatar hakan ta taso.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Sanata Uba Sani ya taimaki Yan Nigeria
Gwamnan ya cigaba da cewa, Gwamnati ta yi amfani da dokiyoyin ta, wurin samar da manyan motocin kashe gobara guda 27, Motocin daukar marasa lafiya, Riijiyoyin burtsatse, da kuma cigaba da gyara sassa daban-daban na hukumar kare afkuwar goba ta jihar.
A karshe Gwamna Mai Mala Buni ya bukaci hukumar kiyaye afkuwar gobara ta kasa baki daya, da ta cigaba da bai wa, ta kwararta ta jihar Yobe cikakken horo, domin cigaba kare rayukar da dukiyoyin al’uma.