Babban Sakataren Ma’aikatar Agaji, Cigaban Jama’a da Kula da Bala’oi, Nasir Sani Gwarzo, ya bukaci gwamnatocin Jihohi da su tabbatar da dokar hana wa nakasa wariya ta shekarar 2018 domin isar da ingantacciyar hidima ga duk masu nakasa a kasar nan.
Ya yi wannan kiran ne a Abuja a wajen bude taron shugabannin da ke da alhakin farfado da nakasassu a Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Shugabannin PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC A Jihar Kogi
Ya yi nuni da cewa, dokar tana neman hada kan nakasassu a fannonin ilimi, kiwon lafiya da zamantakewa da tattalin arziki da hakkokin jama’a da dai sauransu.
Darakta, bukatu na musamman na ma’aikatar, Nkechi Onwukwe, ta ce, “Kamar yadda muka sani, nakasassu (PWDs) sun zama kungiyar jama’a da ke fama da wariya ga al’umma da rashin fahimtar jama’a.”
“Har ila yau, suna fuskantar shingen ɗabi’a daga al’umma, ‘yan uwa da masu ba da sabis, da kuma matsalolin muhalli da sadarwa.”
“Wadannan shingayen ba wai kawai sun rage muryoyinsu da shiga cikin tsara shirye-shirye ba, har ma da samun damar yin ayyuka masu mahimmanci.”
“Haka zalika suna fuskantar rarrabuwar kawuna na tsarin da ke haifar da raguwar matsayi na tattalin arziki da zamantakewa, ƙara haɗarin tashin hankali da nuna wariya, shingen samun ilimi, kiwon lafiya, bayanai da ayyuka da adalci gami da shiga cikin jama’a da siyasa. Wadannan, don haka suna hana su shiga daidai da sauran.”
A wani labarin kuma, Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Ayarin Motocin Sanata Ifeanyi Ubah
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da harin da aka kaiwa ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah.
A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Facebook, tsohon mataimakin shugaban kasar ya jajantawa iyalan wadanda suka jikkata da kuma wadanda aka kashe a harin.