Gwamnatin tarayya ta ce sun sanya ma’aikatan kiwon lafiya a cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon sake ɓullar Ebola a Guinea.
Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce za su sa ido a dukkanin hanyoyin shiga ƙasar domin daƙile cutar da kuma saurin gano wanda ke ɗauke da ita.
Ministan ya tabbatar da cewa; Nijeriya a shirye ta ke ta tura jami’ai domin taimakawa Hukumar Lafiya ta duniya wajen yaƙi da Ebola a Guinea.
Mutum huɗu Guinea ta ce yanzu ya kamu da cutar.
Annobar Ebola da ta ɓarke a 2014 zuwa 2016 ta kashe sama da mutum 11,000 a Afrika.