Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai da gwamnati a yakin da ake yi da cin zarafin ma’aikata da rikice-rikice a wuraren aiki.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, ya yi wannan kiran a ranar Talata, a birnin Tarayya Abuja, a yayin bude wani taron karawa juna sani na masu ruwa da tsaki na kwanaki biyu kan ILO 190 (C190) kan Tashin hankali da Tursasawa da kawar da cin zarafin jinsi (GBV) a wurin aiki.
Ministan, wanda Babban Sakatare a ma’aikatar, Dakta Yerima Tarfa ya wakilce shi a wurin bitar, ya ce Yarjejeniyar 190 ita ce yarjejeniya ta farko ta duniya don amincewa da hakkin kowa da kowa a duniyar aiki ba tare da tashin hankali da cin zarafi ba, da kuma nuna wariyar jinsi.
Ya kara da cewa kawar da cin zarafi da tashin hankali a wuraren aiki ya yi daidai da kudurin Gwamnatin Tarayya na samar da yanayin aiki mai dacewa ga maza da mata a cikin kasar nan, kamar yadda ya dace a cikin kasashen da suka ci gaba.
Ministan ya kuma ce Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen tabbatar da yarjejeniyar ILO 190, da shawarwarin 206 kan Tashin Hankali da Tursasawa.
A cewarsa wannan zai ƙarfafa tsarin hukumomi da na doka da ake da shi domin yaƙar tashin hankali da musgunawa, da wariyar jinsi a cikin ƙasar.