Gwamnatin tarayya ta bayyana fatanta na cewa shawarwarin da suka cimma a taron da suka gudanar da bangarori uku na kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i za su samar da sakamako mai kyau a mako mai zuwa.
Jami’in hulda da jama’a a ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka Mista Olajide Oshundun, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce an cimma wasu yarjejeniyoyin tsakanin gwamnati da kungiyoyin.
Kungiyar malaman jami’o’i ASUU, da manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, kungiyar ma’aikatan jami’a da ba malamai ba, na ci gaba da yajin aiki a halin yanzu.
Kungiyoyin sun fara yajin aikin ne a daidai lokacin da suke bukatar a inganta tsarin jin dadin tafiyar da tsarin jami’o’in, da kyautata yanayin aiki da kuma aiwatar da yarjejeniyoyin ma’aikata daban-daban da suka rattaba hannu da gwamnatin tarayya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2015.
Ministan kwadago da nagartar ayyuka Sanata Chris Ngige ya ce, “Mun yi tattaunawa mai inganci; mun kalli batutuwan da rashin son zuciya kuma muka cimma wasu yarjejeniyoyin, don gamsar da kowa da kowa da ya halarci wurin taron.”
Ngige ya ce an yi taron da ma’aikatar kwadagon ne saboda gwamnati ta hada hannu da wasu masu ruwa da tsaki a yunkurin sasanta rikicin da kungiyoyin.
Wadanda suka halarci wajen taron dai sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa kuma shugaban taron bangarori uku, Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban majalisar addinai ta Najeriya, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, da kuma shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya kuma shugaban NIREC, Rev. Sampson Ayokunle.
Tawagar tattaunawar ta kuma samu ministocin kwadago, kudi, ilimi, shugabannin ASUU, da sauran masu ruwa da tsaki.
A nasa jawabin, Gambari ya koka kan yadda matsalolin da ake fama da su a jami’o’in suka lalata jadawalin karatun daliban Najeriya.