Gwamnatin tarayya ta ce za ta fara aikin gyaran titin Kara zuwa Ogun da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan daga ranar Asabar 3 ga Satumba, 2022.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kwamishinan Sufuri na Jihar Legas, Frederic Oladeinde, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ya samu sanarwa daga ma’aikatar ayyuka ta tarayya kan ayyukan sake gina mashigar Berger-OPIC na babbar hanyar Legas zuwa Ibadan na gaggawar gyara aikin fadada aikin hanyoyin da suka lalace.
“Sanarwar ta bayyana cewa, ana bukatar a gudanar da aikin gyare-gyaren gaggawa a kan hanyoyin da fadada guda uku don kare afkuwar hadurra da lalacewar ababen hawa, don haka akwai bukatar a sanar da mazauna garin da masu ababen hawa a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan,” in ji kwamishinan sufurin a ranar Juma’a.
Karanta kuma: Mutum 4 sun mutu, biyar sun jikkata a kan hanyar Legas zuwa Ibadan
Oladeinde ya ce gwamnatin jihar za ta hada gwiwa da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA), da kuma hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun domin samar da isassun hanyoyin karkatar da ababen hawa tare da ingantaccen tsarin kula da ababen hawa a tsawon lokacin ayyukan gyaran.
Ya shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan a kan wannan hanya a tsawon lokacin gyaran tare da yin hakuri, ya kuma kara da cewa za a dauki matakan dakile matsalolin.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Oladeinde ya nemi hadin kan jama’a tare da jami’an kula da ababen hawa ta hanyar bin dokokin hanya da ka’idojin hanya don hana tafiye-tafiyen da ba za a iya kaucewa ba tare da tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa cikin walwala yayin da aikin gyaran ya kare.
A wani labarin kuma: Sama Da Mutane 1,000 Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Sun Samu Kayayyakin Agaji — NEMA
Akalla mutane dubu daya da ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomi 13 na jihar Katsina a ranar Alhamis din nan ne suka ci gajiyar kayayyakin agaji da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta raba.
Ministar jin kai Sa’adiya Umar Farouk tare da babban daraktan hukumar NEMA Mustapha Kabir Ahmed ne suka mikawa gwamnatin jihar kayayyakin a harabar hukumar ta Katsina.