Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar lura da jiragen kasa ta Najeriya a ranar Alhamis ta sanar da cewa ta sake hada layin jirgin dogo daga Abuja zuwa Kaduna da wasu ‘yan ta’adda suka kai masa hari ta hanyar dasa Bom, a ranar 28 ga Maris, 2022 a Kaduna.
Sanarwar da Hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban Hukumar Fidet Okhiria, ta bayyana cewa an kammala manyan ayyukan layin dogo, inda ta kara da cewa nan ba da jimawa ba za a ci gaba da gudanar da ayyukan layin dogo.
Sanarwar ta kara da cewa, “A kokarin da muke yi na maido da titin Abuja zuwa Kaduna, don ci gaba da aiki cikin gaggawa, hukumar tayi fatan za a lura da sabbin abubuwan da aka sabunta.
Hukumar ta NRC ta bayyana cewa jirgin Loco 2502 da hatsarin ya rutsa da shi (ko da yake bai lalace ba) kuma ya makale a karshen Rigasa saboda rashin hanyar da ta kama a yanzu ta tsallaka zuwa karshen Idu inda aka tafi da ita taron bita don duba yadda ya kamata da kuma kula da ita.
Hukumar ta kara da cewa, “Za a bukaci fasinja su ba da lambarsu ta NIN don tantancewa kafin sayen tikitin jirgin kasa.
Wannan mataki a cewar Fidet, sun samar da shi ne don tattara ingantattun bayanan fasinjan cikin jirgin.