Gwamnatin tarayya ta hana shige da fice tsakanin wasu kasashen Afirika Jaridar Thisday ta ruwaito
Gwamnatin tarayyan Najeriya ta sanar da haba shigowa daga wasu kasashen afirika guda biyar gudun sake yaduwar cutar Covid-19 karo na uku.
Kasashen sun hada da South Africa, Uganda, Nimibia, Rwanda da kuma Zambia.
KARANTA:- Gwamnatin tarayya ta sake tsawaita wa’adin hada Layin waya da lambar NIN
Boss Mustapha ya sanar da haka a wani toron manema labarai jiya a Abuja.
Sannan ya sanar da tsawaita dokar shige da fice da aka saka akan wasu kasashen turawa wadanda suka hada da Turkey, Brazil da Indiya har sai an killace Mutum na tsawon mako biyu kana a bashi damar shigowa.
Yace an kara tsawaita wa’adin har zuwa mako hudu masu zuwa kamin ganin yadda lamarin zai kasan ce.
Yace Kasar South Africa ta sanar da kamuwar mutane dubu dari a cikin sati daya kacal, sannan mutum dubu ashirin a cikin awa ashirin da hudu.
Sannan yaja hankalin mutane kada suyi sake da dokar saboda yaduwar cutar Covid-19 karo na uku ya soma a wasu kasashen.
Ya lissafa manyan Kasashe guda hudu wadanda abun yayi kamari a yankin inda suka hada da America da South Africa da Brazil da kuma Indiya.
Yace dokar da aka sakawa matafiya Yan Najeriya na tsawon wata shida ya kusa karewa.