By Ishaq Dabai
Gwamnatin Tarayya ta hannun Kwamitin Shugaban Kasa PSC kan cutar COVID-19 ta hana sama da ‘yan Najeriya 2,000 da ‘yan kasashen waje yin balaguro zuwa kasashen waje da shiga cikin kasar na tsawon shekara guda, saboda gujewa gwajin cutar Corona PCR a filayen jiragen saman kasa da kasa na kasar.
Manajan abubuwan dake faruwa na kasa NIM na Kwamitin Shugaban Kasa PSC, Mukhtar Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani na ranar Litinin, a Abuja.
Muhammad yace an manna sunayen mutane sama da ‘yan kasa da kuma ‘yan kasashen waje 2,000 a duk manyan cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya inda aka sanya kwararrun likitocin daza su kula da ‘yan Najeriya da’ yan kasashen waje da suka yi balaguro zuwa cikin kasar yayin bala’in cutar COVID-19 karo na uku.
Yace gwamnati ta dage cewa dole ne a kebe fasinjoji, wadanda suka shigo kasar, musamman daga kasashe masu hadari, a wani wurin da gwamnati ta samar, kuma an dakatar da fasfot din wadanda suka ki bin ka’idar na tsawon shekara guda.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kwamitin shugaban kasa PSC a ranar 1 ga Mayu 2021, ta bada Shawarar Balaguro ga fasinjojin dake shigowa Najeriya daga Brazil, Indiya da Turkiyya.inda ya nuna damuwa da shakku kan kara watsuwar ta ga jama’a, a cewar shugaban, Boss Mustapha.
A karkashin matakan, fasinjojin dake zuwa daga wata kasar ko waɗanda suka ziyarci ɗaya daga cikin waɗannan ƙasashe uku a cikin kwanaki goma sha huɗu 14 kafin ziyarar zuwa Najeriya, an buƙace su dasu keɓe masu isowa da kuma dole ne sai sunbi ka’idojin gwaji a wuraren da aka keɓe.