Gwamnatin tarayya ta umurci ’yan fim da su guje wa abubuwan da suka shafi kudin tsafi a cikin fina-finansu.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata ziyarar manema labarai da ya Kai ofishin Daily Trust da ke Abuja.
Ministan ya ce ikirari da wasu mutane da ake zargi da aikata ta’addancin da suka aikata a shafukan sada zumunta na yanar gizo ya karawa Gwamnatin tarayya kaimi wajen ganin ta dauki matakin tsaftace kafafen sada zumunta.
Ya ce, “Da yawa kuma sun zargi Nollywood da nuna al’adar kudin tsafi a wasu fina-finanta, inda suka ce hakan ya yi illa ga matasa masu rauni. Don magance hakan, na umurci Hukumar Tace Fina-Finai ta kasa, da hukumar da aka kafa domin daidaita harkar fina-finai da bidiyo a Nijeriya, da ta yi la’akari da wannan batu yayin gudanar da aikinta na tace fina-finai da bidiyoyi.