By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin gina dam din Okuta mai tsawon kubik miliyan 1.8 a karamar hukumar Baruten ta jihar Kwara.
Hukumar raya kogin Neja ta kasa (LNRBDA) ce ta kaddamar da aikin wanda za a yi aiki kusan sama da hekta 100.
Da yake kaddamar da aikin a karshen mako, Ministan Albarkatun Ruwa, Injiniya Suleiman Adamu, ya ce madatsar ruwan da aka kawo tana cikin 260 da gwamnatin tarayya ta gina a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa, an tsare ruwa mai yawan kubik biliyan 34 a cikin tafkunan dam domin noma da sauran abubuwan amfanin rayuwa.
A cewarsa, duk da kokarin da gwamnati ke yi na inganta samar da ruwan sha ga ‘yan Najeriya, samar da ruwan sha a kasa kusan kashi 70 ne kawai; wanda ke kasa da shirin SDGs na kashi 100 cikin 100 nan da shekara ta 2030.
Ministan wanda ya samu wakilcin Darakta, Ayyuka da Kula da koguna na ma’aikatar, Mista John Ochigbo, ministan ya bayyana madatsar ruwa ta Okuta a matsayin “mahimman kadara ta kasa”.
Ya bukaci al’ummar Okuta wadanda galibinsu manoma ne da su yi amfani da wannan madatsar ruwa domin bunkasa harkar noman rani da akeyi duk shekara.
Manajin Darakta (MD) na LNRBDA, Dr Adeniyi Saheed Aremu, ya ce an fara aikin gina Dam din ne tun a shekarar 2018 domin bunkasa noma da sauran su.
Mai martaba Sarkin Okuta, Alhaji Abubakar Sero Idris, ya bayyana jin dadinsa da yadda madatsar ruwan za ta shiga tarihi a matsayin aikin gwamnatin tarayya na farko da za a fara aiki a garin.
Ya kuma ba da tabbacin cewa al’umma a shirye suke su samar da filaye masu yawa don ci gaban aikin.