Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin titin farko mai tsawon kilomita 66.10 na sabuwar hanyar Gombe zuwa Yola da ake sake ginawa.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Dr Isa Ali Pantami ne ya halarci bikin kaddamarwar a garin Kumo dake karamar hukumar Akko.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: ASUU Ta Kara Tsawaita Yajin Aiki
Ya ce an bayar da aikin sake ginawar ne a shekarar 2014 amma ba a iya farawa ba har sai shekarar 2015, lokacin da aka gyara matsalolin fasaha da ke da alaka da aikin, wanda ya ba masu ginin damar fara aiki.
Pantami ya kara da cewa ya kamata a kammala aikin a shekarar 2019, “amma rashin samar da kasafin kudi da sakin kudade, da kuma cutar COVID-19 ya sa ya zama mai wahala a lokacin da aka kayyade.”
Ministan ya bukaci mazauna jihar da masu ababen hawa da ke bin hanyar da su kare tare da daukar nauyin aikin.
A nasa bangaren, daraktan kula da manyan tituna a ma’aikatar ayyuka ta tarayya, Celestine Shausu, ya ce titin na daya daga cikin kashi na shida na ayyukan hanyoyin da aka kammala kuma an mika shi ga jihohi shida.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce an kaddamar da hanyar ne a matsayin cika alkawuran gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na samarwa ‘yan Najeriya ababen more rayuwa da saukaka rayuwa.
Ya roki a kammala hanyar Numan zuwa Jalingo akan lokaci, wanda ya bayyana a matsayin abin tsoro ga matafiya.
A wani labarin kuma Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yi Fatali Da Wata Bukatar FG Kan Abba Kyari
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta shigar na tasa keyar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da aka dakatar zuwa kasar Amurka.
A hukuncin da ya yanke a ranar Litinin din nan, Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da karar da Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya shigar, bisa hujjar cewa bukatar ba ta cika ba.