Daga: Abbas Yakubu Yaura
Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) a ranar Laraba ta amince da wata sanarwa da ma’aikatar kula da harkokin jin kai, da kula bala’o’i da ci gaban al’umma ta yi na daidaitaccen tsarin gudanar da aiki, don kula da halin farar hula da jin kai na masu neman mafaka daga kasar Kamaru.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce an yi hakan ne domin kiyaye yiwuwar ba da mafaka ga masu tada kayar baya daga kasar Kamaru.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/an-kama-jamiin-kula-da-gidan-yari-kan-%c9%93atan-bindigogi-alburusai/
Ya ce: “Dukkanku kun san cewa saboda tashe-tashen hankula a Kamaru, Najeriya ta ga kwararar ‘yan gudun hijirar Kamaru kuma akwai ka’idoji na asali da za a ba ku matsayin ku na masu neman mafaka.”
Ya ce duk wanda ya fito daga kasar Kamaru da ke neman mafaka a Najeriya dole ne ya fara gamsar da hukuma cewa ya yi watsi da gwagwarmayar amfani da makami kafin a dauke shi ko a dauke ta a matsayin su na masu neman mafaka.
“Har ila yau, akwai wasu daga cikinsu da suka zo ko da sun yi ikirarin sun mika makamansu, suna komawa wani lokaci, don shiga kungiyar ‘yan awaren kasar Kamaru.”
“Don haka abin da muka yi a yau shi ne samar da ingantaccen tsari don tabbatar da cewa wadanda ke da’awar cewa su ne masu neman mafaka a zahiri ba ’yan tada kayar baya ba ne.”
“Wadanda suka kawo wa Najeriya hargitsi ko kuma mutanen da za su zo su kai hare-hare a kan kasarsu cikin kwanciyar hankali a Najeriya.”