Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin hada Rajistar Katin dan kasa da kuma layukan salula da ake yi zuwa ranar 30 ga watan Yunin gobe.
Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan wani taro ta na’ura tsakanin masu ruwa da tsaki kan bangaren sadarwa ciki har da shugaban hukumar sadarwa ta kasa NCC Farfesa Adeolu Akande wanda Ministan Sadarwa da Bunƙasa tattalin arzikin fasahar zamani NITDA wato Dakta Isah Ali Pantami.
Cikin wata Sanarwar haɗin gwiwa daga kakakin hukumar NCC Ikechukwu Adinde da takwararahi na Ma’aikatar Sadarwa sun ce karin wa’adin ya biyo bayan samun shawarwari ne daga masu ruwa da tsaki suka bayar ne na cewa zai taimaka gaa wajen baiwa sauran wadanda ba su yi Rajistar ba.
Sanarwar ta ce sakamakon tsarin da ma’aikatar sadarwar ta kawo ya sa kamfanonin layukan salula da dama sun kara bude rassa a wasu wurare don baiwa jama’a damar hada Katin dan kasar da layukan su.
A tanadin doka sashe na 27 da kuma 29 na kundin hukumar kula da katin dan kasa ya ce tilas ne ko wane dan kasa ya mallaki lambar NIN gabannin shiga wata sabgar gwamnatin.
Ba wai kuma kadai a Najeriya ake da wannan tsari ba, ko da manyan Kasashe irin Amurka da Birtaniya na da su mai Social Security Number da Kuma National Insurance Number