Rahotanni na nuna cewa gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da tsarin nan na ‘babu aiki, babu albashi’ kan malaman jami’o’in kasar da ke yajin aiki.
Idan ba a manta ba, kungiyar malaman jami’a a ta kasa ASUU ta tsunduma yajin aikin mako hudu a ranar 14 ga watan Fabrairu shekarar nan, wanda ta sabunta bayan ya kare.
Jaridar Vanguard ta ce shugaban kungiyar National Association of Academic Technologists Comrade Ibeji Nwokoma, ta malaman jami’a ya tabbatar cewa ba a biya mambobin kungiyar albashinsu na watan Maris ba.
Sai dai Mista Nwokoma ya ce wannan matakin na gwamnati ba zai hana su neman hakkokinsu ba.
A wani labarin Kuma na daban.
Jam’iyyar APC ta fitar da Cikakken Jadawalin gudanar da zaɓen ta
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fitar da Jadawalin ayyuka da jadawalin gudanar da zaɓukan shekarar 2023 mai zuwa.
Jam’iyyar ta ce an yi hakan ne bisa tanadin Dokar zaɓe ta shekarar 2022 kamar yadda aka yi mata kwaskwarima da kuma jadawalin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC.
Idan za a tuna cewa, kwamitin Zartarwa na ƙasa na jam’iyyar APC ya yi taro, tare da mika iko ga kwamitin ayyuka na ƙasa na jam’iyyar.
Bayan wannan cigaba ne Kwamitin zaɓe na APC, ya ƙayyade Naira miliyan 100 na fom domin tsayawa takarar Shugabancin ƙasa da kuma fayyace fam din takarar gwamna da ya kai Naira miliyan 50, sai Majalisar Dattawa Naira miliyan 20, sai kuma Majalisar wakilai Naira miliyan 10, da kuma na majalisar jiha akan Naira miliyan biyu.
To sai dai kuma duk da ƙorafin da jama’a da ɗaiɗaikun ƙungiyoyi da kuma ƴan takara ke yi, jam’iyyar mai mulki ta tsaya tsayin daka kan wannan farashi nata, inda a yanzu ta ke sa ran ganin zaɓen fidda gwani da sauran ayyukan da za ta yi kafin zaɓe.
Haka kuma jam’iyyar ta saki asusu guda bakwai daga bankunan Najeriya daban-daban inda ya kamata masu buƙata su fara yin ajiya.
Naƙasassu da mata da matasa masu shekaru 40 zuwa kasa, ba a sa ran su biya kudin fam din takara gaba daya.
Haka kima, Mata da nakasassu za su sayi fom ɗin Nuna sha’awa ne kawai, yayin da za su sami fom ɗin tsayawa takara kyauta.
Yayin da su kuma matasan za su biya rabin kudin fom na tsayawa takara tare da bayar da cikakken biyan kudin nuna sha’awar karbar fam
Comments 1