Daga: Abbas Yakubu Yaura
Akalla ma’aikatan bogi 23 ne aka gano a ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya da ke Abuja, kamar yadda jaridar PUNCH ta gano.
Hukumar da’ar ma’aikata ta tarayya ta gano ma’aikatan da aka gano takardun aikinsu na bogi ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Ceto ‘Yan Kungiyar Kwallon Kafa 33 Da Aka Yi Garkuwa Dasu A Edo
Don haka ta ba da umarnin a raba mutanen da abin ya shafa daga ayyukan nasu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan, ta koka da yadda ake samun ma’aikatan bogi a ma’aikatu da hukumomin kasar tun farkon fara mulkinta.
A makon jiya ne jaridar The PUNCH ta ruwaito yadda wani ma’aikacin gwamnati a ma’aikatar, Richard Oghenerhoro ya bayar da rahoton kasancewar ma’aikatan bogi a ma’aikatar.
Kwamitin da aka kafa a cikin ma’aikatar a kan lamarin ya ba da shawarar sanya takunkumi ga wanda ya karya dokokin aikin gwamnati.
Wakilinmu a ranar Lahadi ya samu kwafin wasu wasiku daga hukumar FCSC da kuma ma’aikatar da suka tabbatar da kasancewar ma’aikatan gwamnati da takardun aikin yi na bogi.
A daya daga cikin wasikun mai kwanan wata 9 ga watan Mayu, 2022, Daraktan daukar ma’aikata, FCSC, Ibrahim Anjugu, ya umarci babban sakatare na ma’aikatar, da ya tabbatar da cewa an kori ma’aikatan bogi 23 nan take.
An kuma aike da kwafin wasikar zuwa ga ofishin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, ofishin Akanta Janar na tarayya da ofishin babban mai binciken kudi na tarayya.
Wasikar ta ce, “Bayan aikin tantance ma’aikata da hukumar ta yi wa jami’an da aka dauka daga shekarar 2013-2020, an gano nadin wadannan jami’an ma’aikatar ku na bogi ne.
“Wadannan mutanen da suke rike da mukaman ba bisa ka’ida ba saboda wasikun nadin nasu na bogi ne, dole ne a sauke su daga aikin su kuma su mayar da duk wata kadara ko kadarorin gwamnati da ke hannunsu cikin gaggawa.
Wani bincike da aka yi na jerin mutanen da abin ya shafa ya nuna cewa 14 daga cikinsu na cikin Sashen Ayyuka yayin da 9 ke cikin Sashen Gidaje.
A wata wasika mai zuwa ga ma’aikatar, mai kwanan wata 25 ga watan Yuli, 2022, mataimakin daraktan daukar ma’aikata na hukumar, Mayen Gajere, ya bayyana cewa har yanzu hukumar FCSC ba ta samu takardar bin umarnin da aka bayar a baya ba, na a kori wadanda abin ya shafa daga aikin.
Gajere ya rubuta cewa, “An umurce ni da in koma zuwa ga wasikarmu ta farko mai lamba FC,3098/S.203/94 mai dauke da kwanan wata 9 ga watan Mayu, 2022 kan wannan batu da ke sama kuma ina tunatar da ku cewa har yanzu hukumar ba ta samu biyan bukatun ku ga umarnin da ke kunshe a cikin wasiƙar da aka ambata a sama ba.
“Saboda haka, kuna da wannan wasiƙar da aka buƙace ku da ku gabatar da martaninku ko kafin Juma’a, 29 ga watan Yuli 2022.”
Daga nan daraktan daukar ma’aikata na ma’aikatar Aliyu Abdullahi, ya bayar da umarni mai kwanan watan 9 ga watan Agusta 2022, inda ya ce, “An umurce ni da in kawo muku abin da ke cikin wasikun da aka makala da Reference No FC.2039/S.122/1/ 108 kwanan watan 25 ga watan Yuli 2022 da Ref. Mai lamba 3098/Ss.203/94 na ranar 9 ga watan Mayu, 2022 bi da bi kuma in sanar da ku cewa jami’an da aka jera sunayensu a cikin wasikun da aka makala an same su da wasiku na karya.
“Saboda haka, an umurci sassan da abin ya shafa da su sauke jami’an da abin ya shafa daga ayyukansu tare da tabbatar da cewa sun dawo da duk wasu kadarorin gwamnati da ke hannunsu.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi Daraktar yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Blessing Lere-Adams, don jin ko an raba ma’aikatan bogin da ayyukan su, ta ce ba za ta iya tabbatar da cikakken bayani kan lamarin ba.
“Ba zan iya tabbatar da hakan ba kamar yadda zan yi magana da Darakta, Gudanar da Albarkatun Jama’a don tabbatar da duk cikakkun bayanan da suka dace,” in ji ta.