Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton kwamitin jihar Legas da ya binciki kisan kiyashin da aka yi a zanga-zangar #EndSARS a matsayin labarin kanzan kurege.
Ministan yada labarai da al’adu, Mista Lai Mohammed ya bayyana haka a ranar Talata a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Ya ce rahoton da aka mika wa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wani sabon salo ne na yada labaran karya.
Ministan ya cigaba da cewa, a maimakon zama na tsawon shekara guda, kamata ya yi kawai kwamitin ya tattara rahotannin kafafen sada zumunta.
Mohammed ya yi zargin cewa rahoton yana cike da sabani, batanci, rashin daidaito da kurakurai. Don haka ya yi mamakin abun da kwamitin ke nufi da karshensa na “kisa a cikin mahallin,” yana bayyana cewa zai iya zama “kisan gilla.”
Ministan ya bayyana cewa rahoton bai bayar da wata shawara ga wadanda aka kashe a Legas ba, yana mai cewa ba za a iya dogaro da shi ba.
Akwai cikakkun bayanai a nan gaba…