By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayya ta nada manyan jami’ai a sabbin jami’o’i hudu da aka kafa a kasar nan.
Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da nadin ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a Mista Ben Goong.
A cewar sanarwar, Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Babura, Jihar Jigawa ta samu Farfesa Sabo Ibrahim a matsayin mataimakin shugaban jami’ar; Misis Fatima Mohammed – Magatakarda; Malam Ibrahim Alhassan – a matsayin mai kula da kudaden jami’ar; da Dakta Abashe Atiku -Ma’aikacin Laburare.
Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Ikot Abasi, Jihar Akwa Ibom ta samu Farfesa Leo Daniel a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Offiongita Nkang – Magatakarda; Mbobo Frasmus-Mbobo –mai kula da kudi na jami’ar; da Farfesa Philip Akor -Ma’aikacin Laburare.
Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Azare, Jihar Bauchi ta samu Farfesa Bala Audu a matsayin mataimakin shugaban jami’ar, Ali Adamu – magatakarda ; Mohammed Lawan -mai kula da sashen kudin jami’ar da kuma Dakta Bappah Magaj -Liburare.
Sanarwar ta kara da cewa Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya, lla Orangun, Jihar Osun ta samu Farfesa Akeem Lasisi a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Kassim Babamale – Magatakarda; Adelani Oyewale -mai kula da kudi na jami’ar da Bukky Asubiojo -Ma’aikacin Laburare.
Nadin da aka yi an yi shi ne domin saukaka daukar sabbin cibiyoyi cikin gaggawa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a shekarar 2021 ma’aikatar ilimi ta sanar da kafa sabbin jami’o’i hudu domin magance matsalar karancin fasaha da magunguna da abinci mai gina jiki.