Masu nazari da bibiyar harkokin Ƙwadago a Najeriya na ci gaba da sharhi dangane da yunƙurin ƙungiyar na fara yajin-aiki, a dai-dai lokacin da babbar kotun sasanta rikicin ma’aikata ta Najeriyar ta haramtawa ƙungiyar gudanar da zanga-zangar lumana tare da shiga yajin-aikin.
Ƙarin farashin man fetur kusan sau uku cikin shekaru huɗu da gwamnati ta yi, tare da hauhawar kuɗin wutar lantarki, su ne manyan al’amuran da suka sanya ƙungiyar ta NLC ta ayyana a ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar zanga-zangar lumana da kuma tsunduma yajin-aikin gama-gari, domin matsawa gwamnati lamba ta sauya tunani.
Kwamared Sa’idu Bello, tsohon Jami’in ƙungiyar Ƙwadagon Najeriya ta NLC ya ce da yana cikin shugabancin ƙungiyar a halin yanzu, da ba zai ba da goyon bayan shiga yajin-aiki ba.
Bisa ga cewar Kwamared Sa’idu, ” lokacin da Buhari ya fito ya ce duk mutumin da ya shiga cikin gwamnati ya ce a sayar da litar man fetur akan Naira 45, to ya cuci ‘yan Najeriya. To amma yana hawa (mulki) ya ƙara (Farashin) zuwa Naira 145 amma talakawa suka yi shiru,” in ji cewar Kwamared.
https://dimokuradiyya.com.ng/kungiyar-kwadago-za-ta-dauki-mataki-kan-karin-kudin-fetur-da-lantarki/
Sai dai yunƙurin ƙungiyar Ƙwadagon na gudanar da zanga-zangar da shiga yajin-aiki ya haɗu da cikas ne, bayan da wani lauya mai suna Sanusi Musa ya nemi kotu da ta dakatar da yunƙurin na NLC, a madadin wata ƙungiya mai suna Incorporated Trustees Peace and Unity Ambassadors Association.
To amma duk da haka, Kwamared Aliyu Gesto dake zaman tsohon sakataren ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Kano na cewa “gwamnati ta raina ƙungiyar Ƙwadago, saboda ko ba komai tana ganin ita ce ta yi dokokin da take tafiyar dukkan harkokin a Najeriya har da dokokin da suka kafa ƙungiyoyin ƙwadago, saboda haka sun san lagon da za su kama su. Amma kuma duk yadda suke tsammani ba haka abin yake ba.
“Ina mai tabbatar maka cewa ƙungiyar Ƙwadago idan za ta iya yin tsayin daka domin ƙwato wa talakan Najeriya ‘yancinsa, to babu mai iya hana su.”
A cikin shekara ta 2015, ana sayar da litar man fetur a najeriya akan naira 85 ne, amma a yanzu ‘yan ƙasar nan na sayan litar ne kan naira 160 zuwa sama.