Sowore

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gurfanar Da Sowore A Kotu Bisa Zargin ‘Cin Amanar Kasa’

Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, a gaban kotu inda take zarginsa da aikata laifuka biyu wanda ya hada da yunkurin cin amanar kasa da kuma cin amanar kasa.

Lauyoyin gwamnati sun zargi Sowore da aikata wadannan laifuka ne lokacin da ya sake gurfana a gaban wata kotu da ke Abuja, a yau Alhamis domin ci gaba da shari’ar da ake yi masa.

Sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen kamar yadda majiyarmu ta labarto mana.

Haka zalika Bbc Hausa sun labarto cewa; kotun ta ware ranekun 11,12 da 13 ga watan Maris domin yin shari’a a kan wadannan sabbin tuhume-tuhume.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *