• Gwamnatin tarayya ta tsawaita ranar hada katin Dan Kasa da Layin waya.
• Wannan shine karo na 7 da gwamnatin ta ke Kara wa’adin hada lambobin.
• Gwamnati ta ce tayi haka ne domin al’umar kasa su Sami saukin samun numbar katin Dan Kasa.
Gwamnatin tarayya ta tsawai ta wa’adin hada lambar Katin dan kasa wato NIN, da layin waya zuwa ranar 26 ga watan Yulin shekaran nan.
Wa’adin na baya, zai kare ne a gobe laraba 30 gawatan nan da muke ciki. Wanda wannan shine karo na bakwai da gwamnatin take tsawaita wa’adin, tun ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2020, da ta bada mako biyu a kan hada Layin waya da lambar katin Dan Kasan.
Karin dai nazuwa ne bayan wasu masu ruwa da tsaki dake kasar nan sun bukaci gwamnatin da ta kara wa’adin biyo bayan Kara samun sabbin masu rajistan katin zama Dan Kasa a fadin kasar nan.
Bayanin tsawaita wa’adin na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwuiwa da ta sami sa hannun jami’in al’amuran yau da kullun, na hukumar sadarwa ta kasa NCC Dakta Ikechukwu Adinde, da Shugaban hadaka kan al’amuran yau da kullun na Hukumar katin zama Dan Kasa Kayode Adegoke, da su fitar a safiyar yau Talata, ta ce, Gwamnatin tarayya ta amince da tsawaitawar ne, bisa yunkurin ta na ganin al’umar kasar nan, sun sami lambar katin zama Dan Kasa cikin sauki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rukayya Dawayya zata tsaya takara a zeben 2023
A karshe Mataimakin Shugaban hukumar sadarwa ta kasa Farfesa Umar Garba Dambatta, da Babban Daraktan hukumar katin Dan Kasa, Aliyu Azeez sun bukaci Al’umar kasar nan da suyi kokarin ganin sun yi hada lambar katin Dan kasar su da kuma Layin wayar su.
Comments 1