Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da amincewar Gwamnatin Tarayya, na ƙara wa’adin tantancewar haɗa katin ɗan ƙasa da layin waya wato NIN-SIM.
Gwamnatin Tarayya tana kira ga ƴan ƙasa da sauran mutane dasu kammala gudanar da tantancewar tasu kafin ƙarshen shekarar 2021.
Wannan ƙunshe a cikin wata sanarwa da Jami’in Harkokin Al’umma Ikechukwu Adinde na Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, dana Hukumar bayar da katin ɗan ƙasa Mr Kayode Adegoke suka sanyawa hannu.

KARANTA WANNAN LABARIN: An gudanar da Bikin Nadin Sarkin Bare -barin kasar Ghana
Ɗaukar matakin ƙara wa’adin tantancewar, kamar yadda sanarwar ta bayyana ya biyo bayan roƙo da Kamfunnan Layuka da sauran masu ruwa da tsaki, inda suke buƙatar a ƙara wa’adin kwanakin, domin tabbatar dacewa an bi matakin da gwamnati ta ɗauka.
Sanarwar ta ƙara dacewa, ƙara wa’adin kwanakin shine ya bada dama na yiwa ƴan Najeriya rajista wanda suke a ƙauyuka, makarantu, da Asibitoci, da wuraren bauta, da ƴan ƙasar waje, gami da ƙara yawan waɗanda aka yi mawa a Najeriya.
“Akan sake dubi da akayi na nasarar da aka cimmawa, ya nuna cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 66 an haɗa masu layuka da katin ɗan ƙasa”inji sanarwar.
Sanarwar ta kuma kara bayyana cewar, wani kaso na yawan mutane a ƙididdiga na Hukumar NIDB basu yi rajistar ba, wanda hakan ya sanya dole Gwamnatin Tarayya tayi dubi akan haka, tare da yin wani yunƙuri dazai magance matsalar, wanda hakan ya sanya aka ƙara kwanakin.
Haɗa katin ɗan ƙasa da layin waya, na taimakawa Gwamnatin Tarayya na ƙara inganta tattalin arziki na zamani, gami da ƙara inganta yadda za’a magance matsalolin damfara na yanar gizo, tare da taimakon jami’an tsaro.
“Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da ƙara wa’adin haɗa layukan waya da katin ɗan ƙasa domin inganta jindaɗin ƴan ƙasa.