Gwamnatin tarayya ta soke wata sabuwar rundunar tsaro da ke aiki a yankin Kudu maso Yammacin kasar wadda ake wa lakabi da ‘Amotekun’ a ranar Talata.
A cikin wata sanarwa da Mai taimakawa Ministan Shari’ar kasar a fannin yada labarai Dokta Umar Jibrilu Gwandu ya sanya wa hannu ta ce samar da tsaro a fadin kasar aiki ne “na gwamnatin tarayya.”
Sanarwar ta kara da cewa kafa rundunar Amotekun ya saba wa doka, “kudin tsarin mulkin Najeriya ne ya yi dokar da ta kafa rundunar sojin kasar da ta ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaron da aikin samar da tsaro a kasar.”
“Saboda da haka babu wata jiha ko wata kungiya da doka ta bai wa damar kafa wata rundunar tsaro a kasar,” in ji sanarwar.