Gwamnatin tarayya tayi burus da kiraye kirayen da wasu gwamnoni jihohi, da suka hadar da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom da Aminu Masari na jihar Katsina dama sauran mutane da kungiyoyi masu zaman kansu ke yi, cewa Ya kamata mutane su kare kansu daga hare haren da ‘yan bindiga suke kai musu.
Ministan harkokin kula ‘yan sanda, Muhammed Dingyadi shine ya bayyana haka yayin zatawa da manema labarai a ranar Talata a Abuja a wajen taron shekara shekara da ma’aikatar tsaro take yi karo na biyu a shelkwatar tsaro dake Abuja, inda yace gwamnati bata goyan bayan ‘yan kasa su dauki makami dan kare kansu kamar yadda gwamna Ortom da Masari suka fada. Dama sauran wasu daidaikun mutane da suke ganin kowa yana da hakkin kare kansa a ra’ayinsu.
Baya da haka ministan yace ya zama wajibi kiran da ‘yan siyasa suka yiwa Jama’a, ya zama yana kan doka, ta yadda zai bunkasa harkar tsaro a cikin al’umma.
Kazalika ya kara da cewa kalubalen tsaro da ake fuskanta daga ‘yan ta’adda masu yakin sunkuru suna fuskantar tirjiya daga rundunar sojoji.