Gwamnatin tarayya ta tantance mutane kusan 8,800 daga cikin 26,000 da suka nemi tallafin karo karatu a kasashen waje.
Manajan shirin bayar da tallafin karatu na kasashen waje a Asusun Bunkasa Fasahar Man Fetur, Bello Mustapha ne ya bayyana hakan a yau Litinin a lokacin tattaunawa da manema labarai a cibiyar dake Abuja.
Shirin karon karatun PTDF na shekara-shekara yana gudana tun daga 2000 tare da tallafawa Masu son zuwa domin Digiri na biyu, na Uku, da sauran su.
“Musamman, mun tantance kusan mutane 8,800 daga mutane 26,000; muna amfani da wannan ofishin kuma muna amfani da sauran cibiyoyin.
“Mustapha ya ce yayin da tattaunawar za ta dauki tsawon makonni uku a Abuja, jihar Bauchi za ta kasance mako guda saboda karancin masu neman shiga yayin da cibiyoyin Kaduna, Legas, Fatakwal za su dauki tsawon makonni biyu don rufe dukkanin shiyoyin kasar nan shida.
Dangane da adadin mutanen da ake sa ran za a fara shirin na 2022/2023 a watan Satumba, ya ce, “Ina jin a shekarar da ta wuce, mun dauki mutum 3 domin MSC, biyu kuma don digiri na uku, don haka ban san a bana ba ko za mu iya sama da haka.
ku duba kasafin mu kafin in yi tunanin mun fito da zabin karshe.” inji shi.