By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayya ta sake tsawaita wa’adin tantance katin shaidar dan kasa (NIN) akan layukan katin SIM .
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Tun farko dai gwamnati ta sanya ranar 31 ga watan Disamba, 2021, a matsayin wa’adin aikin na karshe.
Sai dai a wata sanarwa ta hadin gwiwa da Dakta Ike Adinde, Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da Mista Kayode Adegoke, Shugaban Hukumar Kula da Shaidar katin dan Kasa (NIMC) suka sanya wa hannu, an sanar da ranar 31 ga watan Maris na sabuwar shekarar 2022 a matsayin sabon wa’adin kwanan wata.
“Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) FBCS, FNCS, FIIM, na fatan mika amincewar gwamnatin tarayya don kara tsawaita wa’adin lambar tantancewa ta katin dan kasa (NIN) – na Tabbatar da bayanan layukan waya (SIM) zuwa 31 ga watan Maris na sabuwar shekarar 2022.”
“Masu ruwa da tsaki sun yabawa Gwamnatin Tarayya kan gagarumin ci gaban da aka samu a yawan masu yin rijistar NIN da kuma kara wayar da kan ‘yan Najeriya da masu zama doka a fadin kasar nan.Ya zuwa ranar 30 ga watan Disamba, 2021, Hukumar Kula da Shaidar katin dan Kasa (NIMC) ta bayar da sama da Naira miliyan saba’in da daya (71m) tare da cibiyoyin yin rajista sama da dubu goma sha hudu (14,000) da aka kafa a fadin kasar nan.
“Bugu da ƙari Hukumar Kula da Shaidar katin dan Ƙasa (NIMC) ta kuma kafa cibiyoyin yin rajista a cikin ƙasashe sama da talatin da ɗaya (31) don kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje. Ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba a cikin bayan na katin dan kasa sama da NIN miliyan 71 na musamman a cikin kankanin lokaci, tare da kusan layukan SIM 3 zuwa 4 dake da alaka da NIN , ya nuna irin kokarin gwamnatin tarayya da al’ummar Najeriya da masu son bin doka kuma wannan hakika gaskiya ne abin yabawa ne.
“Bayan bukatar masu ruwa da tsaki da suka hada da ‘yan kasa,lauyoyi da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, gwamnatin tarayya ta tsawaita wa’adin aikin har zuwa ranar 31 ga watan Maris na sabuwar shekarar 2022. Wannan karin wa’adin zai baiwa gwamnatin tarayya damar kara karfafa nasarorin da aka samu, da kuma hanzarta shigar da ‘yan Najeriya a muhimman wurare kamar lungu da sako, da ’yan kasashen waje, makarantu, asibitoci, wuraren ibada, da rajistar masu zama na doka,” in ji sanarwar.
“Minista, da Mataimakin Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta, da Darakta-Janar/Shugaba na NIMC, Injiniya Aliyu A. Aziz a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya yana mika godiyarsa ga dukkan ‘yan Najeriya da masu ruwa da tsaki bisa jajircewa da goyon bayan da suka bayar wajen samun nasarar aikin. Sun kuma yaba da kokarin da ma’aikatan ke yi na tabbatar da hanyar sadarwar NIN zuwa layukan SIM ba tare da wata matsala ba tare da yin kira ga ’yan kasa da mazauna wurin doka da su kammala aikin yin rajistar tantancewa, ta hanyar sadarwar SIM kafin ranar 31 ga watan Maris 2022”.