A safiyar asabar din nan gwamnatin tarayya ta umarci hukumomi da su tura kayan tallafi zuwa yankunan da ‘yan bindiga suka addaba a jihar Sokoto domin rage musu radadi.
Hakan yana fitowa ne daga bakin Ministar agaji da tallafawa rayuwa marasa karfi Sadiya Umar Farouq, yayin da ta umarci hukumomin dake karkashin hukumarta da su gaggauta kai wa wanda rikicin ‘yan bindigar ya ritsa dasu dauki.
Ta ce hukumomin zasu yi aiki ne tare da hadin guiwar kungiyoyin sa kai na jihar Sokoto domin ganin an taimaki wanda abun ya shafa.
Sadiya tace, hukumarta zata tsaya kai da fata domin taimakon wanda abun ya shafa musamman a wannan lokaci da suke bukatar taimako. https://dimokuradiyya.com.ng/yan-firamare-na-ci-gaba-da-cin-abincin-gwamnati-daga-gidajensu/
“Za a tabbatar da cewa an rage musu radadin harin da ‘yan bindiga suka kai musu ta hanyar basu tallafi”.
Ministar ta bayyana cewa al’ummar da lamarin ya afkawa mutane ne masu son zaman lafiya, kuma basu shiga rayuwa kowa ba.
Ministar ta yi Allah-wadai da kisan da aka yiwa al’ummar wannan yankuna da abun ya shafa kuma ta jajantawa gwamnatin jihar Sokoto game da lamarin.
Har yau, ta jajantawa iyalan wadanda iftila’in ya afkawa tare da nuna goyon bayanta gare su.