By Ishaw Dabai
Hukumar dake kula da kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki tace akwai yiwuwar ta kara kudin wutar lantarki daga 1 gawatan satumba mai kamawa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa karin yazone daga kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO aranar 25 gawatan Agusta.
Sanarwar wacce ta samu sa hannun shugaban kamfanin rarraba wutar hasken wutarki EKEDC, Olumide Anthony Jerome, yace akwai yiwuwar kara kudin wutar lantarki daga 1 gawatan Satumba, wannan karin yazone asakamakon karin da suka samu na kudin fito na SBT na yau da kullum na NERC.
Sanarwar tace karin ya nuna karfin kudin wutar na watan Octoba zai maye gurbin na watan satumba.
Acewar sanarwar sabon karin na Eko DisCo, daga kungiyar abokan cinikaiya su suka bukaci da akara naira 2 na kowanne kilowatts a sa’a guda daga 54.08 zuwa 56.08 kWh sanna zasu samar da wuta ta tsawon sa’oi 20 akowacce rana.
Sannan masu shan wutar lantarkin zasu biya naira 58.94 akan kowanne kwh daga naira 56.94 kwh.