A ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na magance labaran ƙanzon kurege, da maganganun ɓatanci, da ƴan bindiga Dadi, ta ware Miliyan ɗari 104,532,705, domin gano musabbabin hakan.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka samu a cikin kasafin kuɗi na shekarar 2022 ‘, a shafin ofishin kasafin kuɗi na Nigeria.
Ministan yaɗa labarai da Al’adu Lai Mohammed a lokutta da dama, yace ƙasar na yaƙi da masu yaɗa labarun ƙanzon kurege da labarun ɓatanci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Jami’an Kwastam sun sake harbe wani a Katsina
A tattaunawar shi da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa, ya taɓa cewa, Nigeria taje wani mataki da ake amfani da labarun ƙanzon kurege domin a ƙirƙiri yaƙi da gwamnati da jami’an ta.
A ƴan kwanakin baya, Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labaru na Kasa, dake ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labaru da Al’adu, ta bada wata sanarwa ga gidajen talabijin na ƙasa dasu guji yaɗa aikace-aikacen ƴan ta’adda.
A Ƙiyasin kasafin kuɗi da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ya bayyana, an lura dacewa, akwai kimanin Naira Miliyan 55,642,215 da za’ayi amfani dasu wajen wani gangami na wayar wa mutane kai akan tsare-tsare gwamnati ga ƴan ƙasa.
“Sun haɗa da taron wayar da kai akan labarun ƙarya, dana ɓatanci, da faɗan Makiyaya da Manoma da fyaɗe da sauran su.
Ƙiyasin Kasafin kuɗin yace kimanin Naira Miliyan 48,890,490 za’ayi amfani da kuɗin wajen tattaunawa da kafafen yaɗa labaru na waje.