Gwamnatin tarayya ta yanke shawara kan mika Abba Kyari ga kasar amurka, Antoni Janar na Nigeria yace, ya gamsu da cewa babu siyasa cikin zargin da Amurka ke yiwa Abba Kyari Kyari.
DCP Abba Kyari yanzu haka yana tsare hannun hukumar NDLEA kan zargin harkallar hodar Iblis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnati a Kano ta sanya dokar hana hawan babur mai ƙafa biyu a wasu ƙananan hukumomi
Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta amince da bukatar Amurka, na a mika mata dakataccen DCP na yan sanda, Abba Kyari, bisa alakarsa da shahrarren dan damfara Abass Ramon aka Hushpuppi da wasu mutune hudu.
Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana hakan a karar da ya shigar gaban shugaban Alkalan babban kotun tarayya dake Abuja kan tuhumar da ake Masa.
An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022 karkashin dokar Extradition Act. Wannan kara da ya shigar ya biyo bayan bukatar Abba Kyari da wakilin jakadan Amurka yayi a Abuja, kamar yadda jaridar vanguard ta ruwaito.