Ministan harkokin Noma da Raya Karkara, Dr Mohammad Abubakar, ya sake tabbatar wa manoma kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa da na’urori masu sarrafa kansu domin bunkasa harkar noma domin samun dorewar tattalin arziki.
Abubakar ya ba da wannan tabbacin ne a wajen bugu na farko na babban taron noma na Afirka ta Yamma 2022 wanda kamfanin Afrinex West Africa Limited tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki suka shirya a ranar Alhamis din nan a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa taken taron na kwanaki 3 shi ne “Samar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ta hanyar noma da injina.
Ministan ya jaddada cewa taron ya yi niyya ne don inganta injiniyoyi da samar da kudade na Noma, samar da sabuwar kasuwa da hadin gwiwa ga masu baje koli baya inganta ayyukan noma don samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
“Haka kuma ya bayyana shirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na samar da abinci, bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
“Wannan zai baiwa mahalarta damar gabatar da samfuransu da ayyukansu, yin hulɗa tare da manyan masana’antun noma a duk faɗin duniya a dandamali don sabbin haɗin gwiwa.
“Zai sa hannun jari a bangaren noma, samar da dama ga matasa da inganta ci gaban tattalin arzikin kasa ga iyalai,” in ji shi.
A cewarsa, yana da kyau a lura cewa akwai alaka tsakanin ci gaban fasaha da kuma samar da abinci.
“Na’urorin na zamani don samar da abinci ana nufin samar da inganci wajen samarwa da sarrafa su, yayin da manoman Najeriya suka yi amfani da na’urori na zamani a tsawon shekaru kadan.
“Gwamnati tana aiki tare da kamfanoni na cikin gida da na waje don kulla yarjejeniyoyin bangarorin biyu da na bangarori daban-daban, da nufin samar da muhimman injunan noma ga manomanmu.
” Ana sa ran shigo da taraktoci kusan 10,000 da na’urorin sarrafa su 50,000 kuma za a raba wa dukkanin kananan hukumomin kasar nan wanda zai samar da ayyukan yi ga daruruwan mutane.
“Gwamnati na yin duk mai yiwuwa don kara yawan taraktocin kasar nan domin samar da su musamman ga kananan manoma,” inji shi.
Ya kara da cewa, “A cewarsa, bangaren noma shi ne ginshikin bunkasar tattalin arziki da bunkasuwa, noma ne kadai bangaren da ke da albarkatu marasa iyaka kuma ba za mu taba ficewa daga harkar noma ba.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN), Dakta Farouk Rabi’u-Mudi, ya ce wannan shiri abin yabawa ba zai tsaya ba wajen habakawa da samar da albarkatu da habaka tattalin arzikin kasa ba amma kuma zai kawo cikas ga asarar da aka samu bayan girbi mai nasaba da na’urorin ajiya.
“Wannan ci gaban da aka samu a fannin noma babu shakka ya shafi kowa saboda tsadar abinci a kasar nan.
“Ba tare da injina ba, batun hauhawar farashin kayan abinci na iya kara yin tashin gwauron zabi saboda sabanin aikin hannu, tsarin noma ne da ake ba da tallafi, yana da sauri da kuma adana lokaci mai yawa da ake kashewa wajen yin aiki a gona.
“Amfani da aikin hannu akan hecta daya na fili zai kai kimanin Naira 40,000 amma da kayan aikin injina kana yin gona iri daya akan naira 6,000 kacal.
Ya kara da cewa, “Ta haka, ana rage farashin samar da abinci kuma za a rage farashin abinci kai tsaye, haka nan za a rage asarar da aka yi bayan girbi sosai,” in ji shi.
NAN ta ba da rahoton cewa injina wani nau’in kayan aiki ne da yawa da ake amfani da su a aikin gona.
(NAN)