By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar malaman jami’o’i ta sake zargin gwamnatin tarayya da laifin yajin aikin da ake fama da shi a jami’o’in gwamnati.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne, ya bayyana a wata hira da wakilinmu cewa gwamnati tana “kwance” na tsawon watanni takwas bayan ta kammala tattaunawa da kungiyar a watan Mayun shekarar 2021.
DUBA WANNAN LABARIN: Yajin Aikin Ma’aikata Ya Gurgunta Tsarin Ba Da Kiwon Lafiya A Jihar Neja
A cewarsa, ASUU ta jira mataki daga gwamnati amma abin ya ci tura.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ASUU a ranar Litinin, 14 ga watan Maris, 2022 ta sanar da tsawaita yajin aikin gargadi na mako takwas bayan wa’adi na tsawon makonni hudu, wanda ya kare kwana guda.
Da yake magana da Jaridar PUNCH Osodeke ya bayyana cewa kungiyar ta fara yajin aikin na makwanni takwas ne domin baiwa Gwamnatin Tarayya “karin lokaci.”
Ya ce, “Tunanin farko shi ne gwamnati za ta biya dukkan bukatun cikin makonni hudu. Amma da yake gwamnati ta ce ba za su iya biyan bukatunmu nan da mako hudu ba, sai muka ce a ba su makonni takwas. Ba ma son shelanta yajin aiki mara iyaka. Mu yi fatan nan da mako takwas za a hadu domin makarantu su koma yadda suke, kuma a samu ci gaba a tsarin.
“Abin da suka yi shi ne yin alkawari kamar yadda suka yi a baya. Ga membobinmu, idan kun yi alkawuran da ba ku cika ba, don me za mu sake yarda da ku? Idan da a ce gwamnati da gaske take a kan wadannan matsaloli, da a cikin makonni hudu an magance matsalolin.
“Muna cewa a saki farar takarda, a saki asusun farfado da jami’o’i sannan a sanya hannu a kan yarjejeniyar, bai kamata a dauki makonni hudu akan wadannan abubuwan ba idan da gaske suke.
“A shekarar 2021, ASUU ba ta shiga yajin aikin ba, kuma na tabbata kuna sane da hakan. Mun kammala tattaunawa a shekarar 2021, mun tafi yajin aiki? Tsakanin Mayu 2021 da Fabrairu 2022, wato wata takwas, su je su duba abin da muka tattauna; shin mun tafi yajin aiki a wannan lokacin? A’a, amma gwamnati ta yi barci.
“Gwamnati ta kwashe watanni takwas tana barci, lokacin da ASUU ta shiga yajin aikin sai suka fito daga bacci.”
Osodeke ya ce gwamnatin tarayya ba ta da kudi don biyan bukatun kungiyar, “Gwamnatin ta ce babu kudi amma suna da kudin zabe. Tsakanin ilimi da zabe, wanne ya fi muhimmanci? Sun yi titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Jamhuriyar Nijar, shin hakan ya fi ilimi muhimmanci?
“Suna da’awar cewa babu kudi, amma Shugaban kasa ya kara kudin harajin kwastam sai ka ga suna tafiya daga wata kasa zuwa wata kasa. Shin hakan ya tabbatar da cewa babu kudi? Su waye ke amfana daga DTA? Shin ba masu rike da mukaman siyasa ba ne? Amma wanda ya shafi talakawan Najeriya, suna ikirarin ba su da kudi. Ba daidai ba ne; shi ne kawai batun fifiko”.