Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ta na fara aiwatar da wani tsari, wanda a karkashin sa mutane masu bukata ta musamman zasu rabauta da kaso 5 cikin dari na ma’aikatan da gwamnati zata dauka ko kuma ma’aikatu masu zaman kan su.
Ministan Ƙwadago da nagartar ayyuka Chris Ngige ne ya sanar da hakan a a karshen makon nan da muke ciki, a garin Abuja. Yana mai cewa ma’aikatar kwadago zata aike da takardar sanarwa zuwa ga ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu nan da zuwa sati mai zuwa domin suma su fara aiwatar da tsarin.
Ngige na wannan jawabi ne a wajen taron cika shekaru 16 da gidauniyar KPAKPANDO tayi, wadda aka samar da ita domin tallafawa masu bukata ta musamman.
Ministan ya kara da cewa ma’aikatar sa kuma zata cigaba da tallafawa Gidauniyar domin kara yawan wadanda suke tallafawa daga cikin masu bukata ta musamman.
A nasa bangaren shugaban taron kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya ce jihar sa tuni ta zartar da doka kan masu bukata ta musamman a jihar domin ganin sun amfana da kunshi kasafin tsarin mulkin jihar.