Gwamnatin tarayya ta ce ta biya wa Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU dukkan alkawuran da ta daukar mata a baya don ta janye yajin aikin gargadi da ta tsunduma na makonni hudu.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan tsawaita wa’adin yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ta yi da makonni takwas.
Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya yi martanin a wata hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Nwajiuba, ya ce gwamnatin tarayya ta biya dukkan bukatun ASUU, inda ya kara da cewa an saki dukkan alawus-alawus da sauran kudaden kungiyar da aka rike.
“ASUU ta kira taro kuma mun amsa gayyata tare da biyan dukkan bukatunsu, ciki har da alawus-alawus da sauran kudadensu amma ba mu san dalilinsu na tsawaita yajin aikin ba,” in ji shi.