By Abbas Yakubu Yaura
Mataimakan shugaban kasa Yemi Osinbajo (SAN) ya ce wadan da suka kammala karatun digiri dubu 20 ne za su fara shirin biyan kudi a watan Janairun 2022 ta hanyar shirin cigaban Majalisar Dinkin Duniya da hadin gwiwar gwamnatin tarayya.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wajen taron tattaunawa kan manufofin shugaban kasa na kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas na shekarar 2021.
A cewarsa, hadin gwiwar na karkashin shirin Jubilee Fellows na Najeriya ne, da nufin bude hanyoyin magance rashin aikin yi ta hanyar samar wa matasa ‘yan Najeriya 20,000 da suka kammala karatu a duk shekara da basu ayyukan yi na tsawon shekara guda a sassan gwamnati da masu zaman kansu a fadin kasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Laolu Akande, ya fitar a ranar Asabar, mataimakin ya kuma bayyana yadda gwamnatin tarayya ke aiwatar da matakan rage gibin rashin aikin yi da matasan kasar ke fuskanta ta hanyar ayyukan yi.
“Wadannan sun hada da shirin N-Power inda aka dauki matasa ‘yan Najeriya kimanin miliyan 1.5 na tsawon zango biyu da kuma shirin Jubilee Fellows tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar Tarayyar Turai, da sauran abokan hulda na shekara guda. Shirin bai wa matasan Najeriya 20,000 aiki zai fara aiki a watan Janairun shekarar 2022, “a wani bangare na sanarwar.
Osinbajo ya kuma bayyana cewa, hadin gwiwar gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu “dole ne ya inganta samar da kayayyaki da kara kima da kuma kawar da kai daga halin da ake ciki na sarrafa karancin albarkatun kasa don samarwa da samar da karin gasa da dorewa.”
Yace ta hanyar sabon tsarin ci gaban kasa, gwamnatin tarayya na mayar da hankali musamman kan samar da ayyukan yi, da kara kima, da inganta yanayin kasuwanci.
Da yake bayyana yadda za a aiwatar da hadin gwiwar, mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, shirin “yana da niyyar zuba jarin Naira Tiriliyan 348 a tsawon lokacin shirin wanda ake sa ran Gwamnati a dukkan matakai za ta samar da kusan Naira Tiriliyan 49.7 ko kuma kusan kashi 14%, yayin da kuma Ana sa ran kamfanoni masu zaman kansu za su zuba jarin Naira tiriliyan 298 ko kuma kusan kashi 86%.