Ministar agaji da kyautata rayuwa Sadiya Umar Farouq ta ce gwamantin tarayya na shirin ɗaukar waɗanda aka yaye a shirin tallafi na N-Power aiki.
Sadiya ta buƙaci matasan da su ƙara haƙuri kafin fitowar sakamakon ƙoƙarin da ake yi na ganin yadda za a shigar da waɗanda suka cancanta daga cikinsu aikin gwamnati.
“Mun umarci masu kula da shirin tallafa wa matasa a jihohi da su gabatar mana da cikakken jerin sunayen tsoffin ‘yan N-Power da ke sha’awar shiga shirin”.
Sanarwar ta mai ba ta shawara kan yaɗa labarai, Misis Nneka Anibeze, ta ƙara da cewa, “An ba da izinin biyan alawus ɗin da rukunin farko da na biyu da suka kammala shirin suke bin bashi”.
“An riga a gabatar wa ofishin akanta Janar ta tarayya umarnin biyan alawus ɗin watan Yunin 2020 ga rukunin domin ya ƙara dubawa ya biya su.
“Abin da kawai ya rage a miƙa wa ofishin shi ne na biyan alawus ɗin rukuni na biyu na watan Yuli”, inji sanarwar.