Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kudurinta na inganta tsaro a fadin kasarnan. Kwamishinan lura da ayyukan tsaron ‘yan sanda, Alhaji Muhammad Dingyadi, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da tsaro da kuma ingantaccen ilimi ga matasa a duk fadin kasarnan.
Odutayo Oluseyi, mataimakin Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja. Inda ya tabbatar da cewa; Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da kungiyar NANCE wato Kungiyar Kwalejojin ilimin Nijeriya ta kasa suka kai masa ziyara.
Dingyadi ya ce ya samar da tsaro da ingantaccen ilimi su kadai ne kawai za su samar muhalli mai cike da zaman lafiya musamman a kwalejojin ilimi.