Dama dai tuni Nijeriya na da bashin Dala Biliyan 2.4 akan ta, kuma yanzu tana sake neman karin Dala Biliyan 2.5 daga bankin duniya.
Mataimakin shugaban bankin na Afirka, Hafez Ghanem ne ya bayyana hakan a tattaunar da aka yi da shi a garin Abuja, kuma Jaridar Bloomberg ta ruwaito.
A shekarun da suka gabata, Nijeriya ta karbi bashin Dala Biliyan 2.4 daga bankin duniyan in ji Ghanem. “A yanzu haka muna tattauna sabon bashin da Nijeriya ke so na Dala Biliyan2.5bn,” in ji shi.
Nijeriya za ta karbi kudin ne domin Shawo matsalar wutar lantarki a Nijeriya, inda aka ce hakan yana da matukar amfani domin zai jawo masu saka hannayen jari su zuna hannun jari don ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
A halin yanzu Bashin cikin gida na Nijeriya ya kai Dala Biliyan 55.6bn inda bashin waje kuma ya kai Dala Biliyan 25.6bn. Idan zamu tuna, babu dadewa ministar kudi, kasafi da tsari na kasa, Zainab Ahmed, ta ce Nijeriya ba ta da matsalar bashi duk da maganganun masana tattalin arziki akan hauhawar bashin kasar nan.