Majalisar zartaswa na gwamnatin tarayya, FEC ya amince da a kashe naira sama da biliyan takwas domin siyo kayayyaki goma sha biyu ga cibiyar dake dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC domin bunkasa wuraren gwajin cutar korona a kasarnan.
Ministan lafiya, Osagie Ehanire, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a zaman da majalisar zartaswar ta 11 ta yi a shafin Intanet wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnatin shugaban kasa dake Abuja.
Dr Ehanire, ya ce yaduwar cutar korona a tsakanin al’umma ya shafi kananan hukumomi 586, inda ya ce suna yin wani abu domin samar da cibiyar dibar samfuri domin tantance al’ummar dake dauke da cutar korona a dukkanin kananan hukumomin Nijeriya 774.