Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya ce gwamnatin tarayya ta kera na’urar tsaro a kewayen madatsar ruwa ta Zungeru da ake ginawa domin ganin an gaggauta kammala aikin nan da watanni uku masu zuwa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talatar nan lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Sin a Najeriya, H.E. Chui Jianchun, a wata ziyarar ban girma a gidan gwamnati, da ke Minna.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Bello ya ce an shirya tsaron ne a matakai daban-daban domin tabbatar da tsaron ‘yan kasar China da ke aiki a madatsar ruwan da kuma kare wuraren.
Ya kara da cewa duk da dimbin kalubalen tsaro da ake fama da shi a jihar, gwamnatin tarayya na daukar matakan tsaro domin ganin an samu nasarar kammala aikin wanda a cewarsa ya kai kashi 95 cikin 100 na kammala aikin.
Yayin da yake jinjinawa wakilin kasar Sin kan ziyarar, Bello ya koka da yadda wasu masu hakar ma’adanai na kasar Sin ba bisa ka’ida ba suke yi a jihar, yana mai jaddada cewa gwamnati na son yin hadin gwiwa da kamfanonin hakar ma’adanai da aka amince da su a cikin harkokin kasuwanci amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen dakile masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Tun da farko, Jakadan kasar Sin a Najeriya, Mista Chui Jianchun, ya ce ya je jihar ne domin duba matakin da ake kai a madatsar ruwa ta Zungeru.
Mista Jianchun, wanda ya bayyana gamsuwa da aikin da ingancin aikin a madatsar ta ruwa, amma ya yi nadama kan yadda rashin tsaro ya zama koma baya ga kammala aikin a kan lokaci.
Ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi asarar kimanin dalar Amurka miliyan 20 sakamakon tsaikon da aka samu wajen kammala aikin, yana mai ba da tabbacin cewa, tare da tallafin da ake sa ran za a yi a wurin, za a kammala aikin nan da watanni uku masu zuwa.