• Shugaba Buhari ya amince a zauna da kamfanin Tuwita domin yin sulhu.
•Lai Mohammed shine zai jagorancin tawagar kasar nan, a zaman da za ayi.
• Gwamnatin tarayya dai ta dakatar da kamfanin Tiwita ne sakamakon wasu aiyuka da ake yi dake barazana ga dorewar Nijeriya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da tawagar kasar nan, su zauna zaman sulhu da na kamfanin Tuwita, biyo bayan dakatar da amfani da shafin a Nijeriya da gwamnatin tarayya ta yi.
Ministan yada labarai da al’adu na kasa Lai Mohammed ne, ya sanar da amince war, wanda kuma shine zai jagorancin tawagar a zaman sulhun.
Daga cikin wadanda suke tawagar zaman akwai, Antoni janar na kasa, Ministan shari’a, Ministan sadarwa, Ministan kasashen waje, Ministan aiyuka da gidaje, Ministan kwadago, da kuma wasu daga cikin hukumomin gwamnatin tarayya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jaruma Farida Jalal ta yi tufka-da warwara
Idan za a iya tunawa, dakatar da kamfanin Tiwita da gwamnatin tarayya ta yi a Nijeriya, ya biyo bayan wasu aiyuka, da ake yi a kafar sadarwar, wanda ke barazana ga hadin kan kasar nan.
Kuma kamfanin Tiwita ne ya rubutawa shugaba kasa Muhammadu Buhari takardar bukatar zaman sulhu, domin yanje dokar da ya sanya, na dakatar da amfani da kamfanin a Nijeriya.