Gwamnatin tarayya ta ziyarci jihar Kano da zummar farfaɗo da masana’antun da suka durƙushe a jihar domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.
Ministan masana’antu da kasuwaci da zuba jari, Otumba Adeniyi ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar ma’aikatarsa domin ziyartar Sarkin Kano, Mai Martaba Aminu Ado Bayero a fadarsa.
Ministan ta bakin Daraktan tsare-tsare na ma’aikatar, Tijjani Babura ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta fara farfaɗo da masan’antu a faɗin ƙasar nan domin samar da ƙarin ayyukan yi da ƙarin kuɗaɗen shiga.
https://dimokuradiyya.com.ng/osinbajo-ya-jagoranci-zaman-kwamitin-tattalin-arziki/
Ya ce baya ga farfaɗo da masana’antun gwamnati za ta kuma lura da gudanar da su duk da cewa tana fama da matsalar ƙarancin kuɗaɗe.
Da yake mayar da jawabi, Mai Martaba Sarkin Kano ya buƙaci tawagar gwamnatin tarayya da ta yi aikin cikin hanzari tare da tabbatar da aiwatar da sakamakon binciken da suka yi.
Sarki Aminu Ado Bayero ya jaddada muhimmancin farfaɗo da masana’atun da ke Kano wajen haɓaka tattalin arziki a yankin yammacin Afirika.