Taron Kwamitin Tattalin arziki na ƙasa ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta biya kuɗin rigakafin Covid-19 miliyan 40.
Yemi Osinbajo ya bayyana cewar rigakafin zai iso ƙasar kashi-kashi a tsakanin watan Oktoba na shekarar 2021 da watan Janairu 2022.
Wannan na daga cikin nasarar da aka cimmawa tsakanin kwamitin tattalin arziki da kwamitin Shugaban ƙasa akan cutar Covid-19, wanda Gwamnan Jahar Delta Dr Ifeanyi Okowa ya jagoranta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Damfara ta yanar Gizo guda 12, sun shiga Hannun Hukumar EFCC a Ibadan
Babban mai taimakawa mataimakin shugaban ƙasa akan kafafen yaɗa labaru Laolu Akande ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar.
Acewar Osinbajo, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya na gina cibiyar samar da na’urar taimakawa lumfashi a faɗin jahohi 36 na ƙasar, amma jahohi 6 aka baiwa cilinda ta taimakawa lumfashi a halin yanzu.
Yace yanzu an sanya Nigeria a cikin ƙasashe 50 dake da kayyakin lafiya.
A cewar rahoto akan cutar Covid-19, wanda Darkta-Janar na Hukumar kula da manyan cututtuka Dr. Ifedayo Adetifa a halin yanzu akwai mutane dubu 9,520 dake fama da cutar, a yayinda mutane dubu 2,761 suka mutu.
Akan ɓarkewar cutar Kwalara, Adetifa yace akwai mutane 88,704 da suke fama da cutar a faɗin jahohi 31 da Babban Birnin Tarayya Abuja, a yayinda mutane dubu 3,208 suka mutu.