Mahukumta a kasar Turkiyya a ranar Asabar sun bayar da umurnin garkame sojoji 47 bisa zargin suna da hannu wajen yunkurin juyin mulki a kasar da ya so ya auku a shekarar 2016.
Jami’an tsaron ‘yan sanda a kasar sun kaddamar da hare-haren samame a yankuna akalla 40 na kasar domin cafke wadanda ake da zargi da hannu wajen yunkurin juyin mulkin kamar yadda ofishin shigar da kararraki da ke yammacin garin Izmir ya bada umurni.
Rahotanni daga NTV sun labarto cewa; tawagar ‘yan sandan suna rike da mutum 36 da ake zargi.
A ranar Talata ne, aka kaddamar da wani samame a yankuna 70, inda aka cafke sojoji 141 ciki harda sojojin da suke kan aikinsu, bisa zarginsu da yunkurin juyin mulkin da aka zargi Malamin nan dan kasar Turkiyya amma mazaunin Amurka, Fethullah Gulen da yunkurin yi.
Gwamnatin Turkiyya ta zargi Gulen da yunkurin juyin mulkin a cikin watan Yulin 2016, inda mutum 250 suka rasa rayukansu, inda yanzu Turkiyyar ke ta kokarin ganin an dawo mata da shi kasarta domin ta hukunta shi.