Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Yobe ta hannun ma’aikatar ilimi ta asali da sakandire ta jihar ta umurci shuwagabanni da masu mallakar makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da su hada kai da malamansu domin ganin daliban da suka kammala karatun su na shekarar karshe ba su shiga ayyukan da suka shafi zamantakewa ba.
Kwamishinan Ilimi na asali da Sakandare na Jiha, Dokta Muhammad Sani Idriss ne ya ba da wannan umarni a wata takarda mai suna: “SHIGAR DA BATA DACE BA DA MUNANAN DABI’U DA AYYUKAN DALIBAN SHEKARAR KARSHE DA SUNAN BUKIN KAMMALA KARATUN”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikici Na Neman Ballewa: China Ta Harba Makamai Masu Linzami
Ya bayyana a cikin da’awar cewa ba za a amince da irin wannan bukukuwan da dalibai ke nuna munanan dabi’u da ayyukan da suka saba wa akida da al’adu da zamantakewar al’umma ba.
“Wani abin da ake kira ranar markers, inda ɗalibai suke rubutawa da yayyaga rigunan su da kuma shiga cikin lalata da yara maza da mata ba wai kawai ya saba wa imaninmu na addini ba ne amma lalata ce, kuma ba za a amince da ita ba.
“Ma’aikatar ba za ta nade hannunta ta kalli dalibanmu suna nuna rashin da’a da sunan bikin yaye daliban ba,” Kwamishinan ya yi gargadin.
Ya jaddada cewa akwai wasu hanyoyin da ake yarda da su na nuna farin ciki wadanda ba su saba wa al’adar al’umma ba.
“Ma’aikatar ba za ta yi jinkirin sanya takunkumi ga duk wata makarantar da aka samu ta ba dalibansu damar yin irin wannan aikin ba”, in ji shi.