Daga Muhammad Gambo Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce bayyana shirin gwamnatinsa na kirkiro wasu kwamitoci na agajin Gaggawa a Kananan hukumomin jihar domin kai daukin gaggawa yayin da iftila’i ya faru.
Gwamna Buni ya bayyana haka a jiya Litinin, lokacin da ya kai ziyara ga shelkwatar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA).
Yace Kwamitocin zasu dinga bayar da taimakon farko ga wadanda iftila’in wata annoba ya shafa, a daukacin kananan hukumomin jihar, kafin hukumar bada agajin gaggawa ta jiha ta isa.
Gwamnan yace za’a karfafa kwamitocin da kayan aiki ta yadda zasu iya agazawa al’umma a lokacin da ya dace.
“Wadannan kwamitoci zasu kasance hanyar bayar da agajin farko ga wadanda iftila’i ya shafa a fadin jihar”, inji Gwamnan Yobe.
Da yake nasa jawabin, Babban Daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed, ya yabawa Gwamna Mai Mala Buni kan wannan yunkuri.
Yace jihar Yobe ta zamo zakaran gwajin dafi a fannin bada agajin gaggawa a fadin Nigeria, wanda hakan abun koyi ne ga sauran jihohin kasar.
Daga bisani, Daraktan ya nada Gwamna Buni a matsayin Jakadan hukumar wato ambasadan NEMA a bangaren jinkai.
A yayin ziyarar, Gwamna Mai Mala Buni yana tare da Kwamishinan Ma’aikatar kudade, Alhaji Mustapha Musa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Yobe Alh. Abdullahi Yusuf da Shugaban Karamar Hukumar Potiskum, Alhaji Salisu Mukhtari.