Gwamnatin tarayya ta raba naira milyan 65 ga mata mabukata a karamar hukumar Guri, ta Jihar Jigawa, a karkashin shirin nann na, Conditional Cash Transfer (CCT) scheme.
Shugaban shirin a yankin, Alhaji Abubakar Dan-Barde, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Guri, ranar Asabar.
Ya ce kowacce daga cikin matan da suka amfana da shirin sun sami tallafin naira 10,000 a watannin Yuli da na Agusta.
Dan-Barde ya ce an zakulo matan ne daga mazabun, Garbagal, Kadra, Matarababba, Lafiya, Margadu, Dawa, Musari, Guri, Adyani da Abunabu, na yankin.
Ya yi nuni da cewa, shirin ya tallafi mata matalauta masu yawa inda suka fara aiwatar da ‘yan kananan sana’o’in su da za su iya dogaro da kansu.
Sauran kananan hukumomin da aka zaba domin gudanar da shirin na CCT a cikin Jihar sun hada da, Kaugama, Guri, Gwiwa, Jahun, Kiyawa, Miga, Roni da Taura.