Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya dakatar da Sarkin Birnin ‘Yandoto na karamar hukumar Tsafe, Alhaji Aliyu Marafa, biyo bayan nadin sarautar da ya yiwa shugaban ‘yan fashi, Ado Alero.
A ranar Asabar ne Sarkin ya nada Alero a matsayin mukamin Sarkin Fulani.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/peter-obi-baba-ahmed-sun-gana-da-obasanjo/
Daukar matakin baiwa sarkin ‘yan fashin mukami ya ta’allaka ne a kan muhimmiyar rawar da ya taka a wani shirin samar da zaman lafiya da aka yi kwanan nan tsakanin masarautar da ‘yan bindigar da ke addabar karamar hukumar Tsafe.
Sai dai a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe Sardauna ya fitar, gwamnatin ta nisanta kanta da duk wasu matakai tare da sanar da dakatar da sarkin nan take.
Ya nada Hakimin ‘Yandoto Alh. Mahe Garba Marafa, wanda zai jagoranci al’amuran masarautar.
Gwamnatin ta kuma kafa wani kwamiti mai Mutane shida karkashin jagorancin Yahaya Chado Gora domin gudanar da bincike kan lamarin da ya kai ga matakin da sarkin ya dauka.
A Wani Labarin Kuma Peter Obi da Datti Baba-Ahmed sun gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Lahadi.
Tsohon gwamnan Anambra kuma tsohon dan majalisar wakilai ne ke neman shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP) a zabe mai zuwa.
Obasanjo ya tarbi ‘yan takarar na 2023 a gidansa dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Har ila yau, akwai babban Fasto na Trinity House, Ituah Ighodalo, mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya.
Abokin Obi kuma tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya, Oseloka Obaze ya yada hotunan taron a shafukan sada zumunta.
Obaze ya kasance dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan Anambra na 2017.
An yi imanin cewa jam’iyyar na cikin neman shawarwarin gabanin babban zaben shekara mai zuwa.